Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - 'WAA' na kasar Iraki ya bayyana cewa jami’an tsaron kasar sun kama wadannan mayakan Daesh ne tare da taimakon jami’an gwamnatin lardin wadanda suke sanya ido a kan ayyukan yayan wannan kungiyar tun da dadewa.
Labarin ya kara da cewa ana gudanar da ayyukan bibiyar wasu sanannun 'ya'yan wannan kungiyar don kama su a cikin kasar, ta hanyar da dokokin kasar suka tanadar kuma an sami nasara. kan kungiyar tun shekara ta 2017, amma har yanzun akwai wadanda suke kai hare-haren ta’addanci daga cikinsu a boye a cikin kasar.
342/